Shirin dai wani tsari ne da gwamnatin ta bullo da shi a matsayin wani muhimmin tsari da zai taimakawa wadan da za su kakkafa kananan masana'antu da kasuwanci a kasar.
Baki daya manufar wannan shiri shi ne domin bunkasa bangaren kamfanoni masu zaman kansu a matakin farko don ciyar da harkokin kasuwanci gaba da samar da guraben ayyukan yi ga matasan kasar Ghana, domin su samu hanyoyin da za su bunkasa kasuwancinsu.
Akufo-Addo ya ce, shirin zai kara baiwa sabbin nau'ikan kasuwanci damar bunkasuwa kuma zai samar musu hanyoyin samun jari da yadda kasuwancinsu zai bunkasa, da ba su kariya a lokacin da ake fama da rikicewar sha'anin cinikayya a shekaru da dama a kasar.
Shugaban na Ghana ya ce, shirin zai taimaka wajen kara hadewa bangarorin kasuwancin waje guda domin samun bunkasuwa da samar da ayyukan yi masu yawa a matakai na tarayyar kasar.(Ahmad Fagam)