in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ana fuskantar karancin allurar riga kafin cutar shan inna a kasar Ghana
2017-07-13 09:40:54 cri
Kasar Ghana na fuskantar karancin alluran riga kafin cutukan shan inna da kyanda a wasu lardunan dake fadin kasar.

Rahotanni sun bayyana cewa, wasu daga cikin asibitoci a kasar na fama da karancin alluran riga kafi, wadanda ke cikin jerin magungunan da ake ba yara don kare su daga muggan cutuka.

A cewar rahotannin, gazawar Ghana na biyan kudin magungunan da ta karba a bara daga asusun kula da kananan yara na MDD wato UNICEF, shi ne ya haifar da matsalar, wanda ake ganin za ta shafi lafiyar yara 'yan kasa da shekaru biyar idan ta ci gaba a haka.

Darakta Janar na hukumar lafiya ta Ghana Anthony Nsiah-Asare, wanda ya tabbatar da karancin alluran, ya ce hukumarsa na sa ran isar alluran cikin kasar a mako mai zuwa, bayan gwamnati ta fitar da dala miliyan 10 don sayen alluran da za a yi amfani da su cikin shekara guda daga UNICEF. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China