in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban kasar Kenya ya lashi takobin fatattakar kungiyar Al Shabaab
2017-07-18 11:13:57 cri
Shugaban Kasar Kenya Uhuru Kenyatta, ya lashi takobin fatattakar mayakan kungiyar Al-Shabaab wadanda ke kashe mutane a yankin Lamu, ya na mai cewa za a tunkari mayakan da muggan matakai.

Uhuru Kenyatta wanda ya bayyana haka lokacin da ya je gamgamin siyasa a yankin Lamu, ya kara da cewa, dole ne su yi maganin 'yan tada kayar bayan, ya na mai cewa ba shi da wata nadama kan tsauraran matakan da gwamnati ke dauka.

Baya ga wannan, shugaban ya kuma yi alkawarin ci gaba da gudanar da ayyukan more rayuwa domin raya kasar. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China