in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Amurka ta yi gwajin na'urar kakkabo makamai masu linzami
2017-07-31 11:14:10 cri
A jiya ne hukumar kula da harkokin sojan Amurka, ta sanar da cewa sojojinta sun yi gwajin na'urar kakkabo makamai masu linzami.

Wata sanarwa da aka rabawa manema labarai ta nuna cewa, an gudanar da wannan gwaji wanda hukumar tsaron makamai masu linzami ta kasar Amurka (MDA) da rundunar sojojin Amurkan suka gudanar cikin hadin gwiwa cikin nasara.

Hukumar tsaron makamai masu linzamin ta ce jirgin harba makamai masu linzami na soja samfurin C-17 ne, ya harba makami mai linzami mai cin matsakaicin zango a sararin tekun Fasifik, wanda daga bisani na'urar kakkabo makamai masu linzami sanfurin THAAD da aka girke a yankin Kodiak na Alaska dake Amurka ya gano ya kuma kakkabo shi.

Sanarwar ta ce, an gudanar da gwajin ne ta yadda na'urar THAAD din za ta iya gano duk wata barazana daga irin wadannan makamai masu linzami da aka harba. (Ibrahim Yaya)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China