in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Dakarun saman kasar Amurka sun harba makami mai linzami karo na hudu daga sansanin Vandenberg a wannan shekara
2017-08-03 10:04:53 cri
A jiya ne sojojin saman kasar Amurka suka harba makami mai linzami karo na hudu a jere a wannan shekara daga sansanin sojojin saman kasar na Vandenberg dake California.

Wata sanarwar da sashen kula da kai hare-hare na kasa da kasa na sojojin saman Amurkar ya wallafa a shafinsa na intanet, ya ce harba makamin ba shi da nasaba da gwajin makami mai linzami na baya-bayan nan da kasar Koriya ta Arewa ta gudanar. Sanarwar ta ce, gwajin ya kara tabbatar da tsaron makamin nukiliyar Amurkar, kana Amurkar za ta iya gano tare da wargaza duk wasu hare-hare da aka yi niyyar kai mata tare da kewayenta.

Bayanai na nuna cewa, yanzu haka Amurka ta girke kimanin makamai masu linzami 450 a sashen kai hare-hare na rundunar sojojin saman kasar, inda za ta rika harba su daga sansanin Vandenberg don tabbatar da ingancinsu.

Gwajin makami mai linzami na baya-bayan da Amurka ta gudanar na zuwa ne a yayin da ake kara fuskantar zaman tankiya tsakanin Amurka da Koriya ta Arewa, 'yan kwanaki bayan da kasar Koriya ta Arewa ta yi nasarar gwajin makami mai linzami da zai iya fadawa wata kasa a ranar Jumma'ar da ta gabata. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China