A watan Sabumban shekarar 2014 ne gwamnatin Habasha ta kebe kudi dala miliyan 100 domin kafa kamfanin samar da wutar lantarki mai amfani da bola a wajen birnin Addis Ababa, hedkwatar kasar Habasha, a wani mataki na kare muhalli. Kamfanin Sin na CNEEC ne ya kafa wannan kamfani, kuma yana aiki ne da duk na'urori da kuma ma'aunin kasar Sin, da zummar shigar da fasahohin kasar a fannin kiyaye muhalli zuwa nahiyar Afirka.
Bayan da kamfanin ya fara aiki, a kowace rana zai kawar da shara ton 1280. A sa'i daya kuma, a kasancewarsa kamfanin samar da wutar lantarki irinsa na farko a Afirka, ya samar da sabuwar hanyar raya biranen kasashen Afirka.(Fatima)