Wata majiya daga ofishin hukumar kula da harkokin zuba jari ta kasar Habashan ko EIC a takaice, ta shaidawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua hakan a Juma'ar nan.
Majiyar ta ce cikin wadannan guraben ayyukan yi, akwai sama da 19,000, wadanda suka jibanci fannin sarrafa kayayyaki, wanda hakan ya sanya Habashan shigewa gaba a fannin jawo jari daga kamfanonin Sin, sama da sauran takwarorin ta na kasashen nahiyar Afirka. Sauran sassan da suka fi samun tagomashi dai sun hada da na gine gine, da kuma na raya harkokin noma.
Wasu alkaluman kididdiga da ma'aikatar harkokin wajen kasar ta Habasha ta fitar, sun nuna cewa, Sinawa sun zuba jarin da yawan sa ya kai dalar Amurka kusan Biliyan 4 a kasar ta Habasha, cikin shekaru 20 da suka gabata. Hakan a cewar hukumar, ya samar da nau'o'i daban daban na guraben ayyukan yi sama da 111,000 ga al'ummar kasar.