Kakakin ma'aikatar harkokin wajen Habasha ya bayyana a jiya Jumma'a cewa, wa'adin fitar bakin haure daga cikin Saudiyya zai cika nan bada jimawa ba wato a gobe Lahadi 23 ga wata.
A halin yanzu, gwamnatin kasar Habasha na kokarin samar da takardu da ababen hawa ga 'yan asalin kasar wadanda suke aiki a Saudiyya ba bisa doka ba, don ba su damar komawa gida lami-lafiya.
Kakakin ya kara da cewa, baya ga mutane dubu 65 wadanda suka riga suka koma gida, akwai sauran wasu 'yan Habasha sama da dubu 60 a Saudiyya, wadanda ke jiran komawa gida.
An yi hasashen cewa, akwai bakin haure 'yan asalin Habasha kimanin dubu dari hudu a Saudiyya, wadanda akasarinsu ke aikin bada hidima gami da gine-gine.(Murtala Zhang)