Mataimakiyar shugaban kasar Inonge Wina, ta ce Gwamnati da hadin gwiwar masu ruwa da tsaki, kamar bankin duniya da bangarori masu zaman kansu, za ta aiwatar da sauye-sauye a tsarin kasuwanci da nufin saukaka matakan yin kasuwanci a kasar.
Kafar yada labarai ta kasar ta ruwato cewa, a jawabin da ta gabatar yayin taron saukaka harkokin kasuwanci a kasar na 2017 da ya gudana a birnin Livingstone dake kudancin kasar, mataimakiyar shugaban kasar ta Zambia, ta ce gwamnati ta bijiro da jerin sauye-sauye dake da nufin magance kalubalen da bangarori masu zaman kansu ke fuskanta, tana mai cewa za kuma a ci gaba da gudanar da sauye-sauyen. (Fa'iza Mustapha)