in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin da Indiya sun kulla yarjejeniyoyin hadin gwiwa guda 24
2015-05-15 18:24:10 cri
Bayan ganawar firaministan kasar Sin Li Keqiang da takwaran aikinsa na kasar Indiya Narendra Modi a nan birnin Beijing a yau Jumma'a, jami'an biyu sun kuma halarci wani bikin sanya hannu na kulla yarjejeniyoyin hadin gwiwa guda 24 a tsakanin kasashen biyu.

Fannonin da wadannan yarjejeniyoyin suka shafa sun hada da layin dogo, hako ma'adinai, ba da ilmi, fasahar sararin samaniya. Sauran sun hada da musayar siyasa da harkokin shiyya-shiyya da dai sauransu.

Kaza lika, a fannin musayar harkokin shiyya-shiyya, kasashen biyu sun kulla dangantakar abokantaka a tsakanin birane guda takwas, watau lardin Sichuan na kasar Sin da lardin Karnataka na kasar Indiya, birnin Chongqiang na kasar Sin da birnin Chennei na kasar Indiya, birnin Qingdao na kasar Sin da birnin Hyderabad na kasar Indiya, da kuma birnin Dunhuang na kasar Sin da birnin Aurangabad na kasar Indiya. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China