Sana'ar kiwon shanu na kara kyautata zaman rayuwar al'ummar gundumar Tuokan ta garin Tiandeng dake jihar Guangxi ta kasar Sin. Wannan wuri na fama da matsalar kwarara hamada da zaizayewar laka, kuma ba'a iya gudanar da ayyukan gona na zamani.
Kiwon shanu, ya zama wata sana'ar gargajiya a wurin.
A 'yan shekarun nan, ana kara habaka wannan sana'a, inda har ta taimaka sosai wajen fitar da jama'a daga zaman talauci.(Murtala Zhang)