Jami'in yankin Nelson Marwa wanda ya tabbatar da hakan, a daidai lokacin da aka fara kai wannan hari a yammacin jiya, ya ce, zai a ci gaba da kai hare-haren duk da adawar da wasu 'yar kasar ta Kenya ke nuna kan wannan mataki.
Wannan hari dai na zuwa ne kwana guda bayan da gwamnati ta ayyana dokar hana fita a yankin, a wani mataki nan a magance hare-haren da mayakan ke kaiwa.
Marwa ya ce dokar hana fitar da gwamnatin ta sanya a yankin na Lamu, da kogin Tana da yankunan Garissa a ranar Asabar, zai ci gaba kafada da kafada da harin da ake kaiwa, don ganin a kawar da mayakan daga dajin na Boni. (Ibrahim)