in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Amurka ta kafa shinge na cinikayya tsakaninta da Rasha, in ji Medvedev
2017-08-03 10:54:22 cri
Firaministan kasar Rasha Dmitry Medvedev, ya bayyana cewa Amurka ta ayyana sanya cikakken takunkumin kasuwanci tsakaninta da Rasha bayan da Amurkar ta amince da sabuwar dokar a ranar Laraba.

Da ma dai a farkon wannan watan ne kudurin dokar ya samu amincewar majalisar dokokin kasar Amurka, duk kuwa da bukatar da gwamnatin Trump ta nema na rokon majalisar ta yi sauye-sauye kan dokar sakamakon alakar dake tsakanin Amurkar da Rasha.

A cewar Medvedev, sakamakon daukar wannan mataki, kasar Rasha za ta ci gaba da harkokinta na raya tattalin arziki da ci gaban al'umma, za ta dogara ne da kanta inda kuma za ta kauracewa dogara da shigo da kayayyaki daga yammacin duniya.

Haka zalika a ranar Laraba, ma'aikatar harkokin wajen Rasha ta nuna rashin jin dadinta game da amincewa da dokar, kana ta kalubalanci kakaba mata sabon takunkumin da Amurkar ta yi, inda ta bayyana cewa mataki ne mai cike da hadari kuma babu hangen nesa game da daukar wannan mataki.

Domin mayar da martani game da sabon takunkumin da Amurkar ta sanya, shugaban kasar Rashar Vladimir Putin a sanar a ranar Lahadi ya sanar da cewa, za'a rage jami'an diplomasiyya na Amurka dake kasar Rasha kimanin 755 daga ranar 1 ga watan Satumbar wannan shekara. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China