in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sabbin takunkuman Amurka za su kara lalata dangantakarta da Rasha
2017-07-27 09:59:33 cri
Shugaban kwamitin kula da harkokin waje na Majalisar dokokin Rasha Leonid Slutsky, ya ce sabbin takunkuman Amurka zasu kara lalata dangantakar dake tsakanin Moscow da Washington, wanda da ma ta yi tsami.

A jiya Laraba ne Kamfanin dillanci labarai na Sputnik, ya ruwaito Leonid Slusky na bayyana cewa, fadada takunkuman zai kawo nakasu ga yiwuwar farfado da dangantaka tsakanin Rasha da Amurka, tare da kara dagula lissafi a nan gaba.

A ranar Talata da ta gabata ne, da kuri'u 419, majalisar wakilan Amurka ta amince da wata sabuwar doka, wadda za ta kakabawa Rasha takunkumai da suka mai da hankali kan bangarorin tsaro, ayyukan sirri da hakar ma'adanai da makamashi da kamfanonin shimfida layin dogo da kuma dai na harka da bankunan kasar.

Shi ma a nasa bangaren, Konstantin Kosachev, shugaban kwamitin kula da harkokin waje na Gwamnatin Rasha, ya wallafa a shafinsa na Facebook cewa, babu makawa, dangantaka tsakanin Moscow da Washington zai kara tabarbarewa, kuma Rasha za ta shirya mai da martani mai zafi ga sabbin takunkuman.(Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China