in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasashen Sin da Rasha sun yi alkawarin kara yin hadin gwiwa kan harkokin kasa da kasa
2017-05-26 10:00:02 cri
A jiya ne kasashen Sin da Rasha suka amince su zurfafa hadin gwiwa a tsakaninsu a fannonin daban-daban, a wani mataki na yin aiki tare da nufin tunkarar harkokin da suka shafi kasa da kasa.

Shugaba Vladimir Putin na kasar Rasha ne ya bayyana hakan yayin ganawarsa da ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi a fadar Kremlin lokacin da ya kai ziyarar aiki kasar ta Rasha.

Ya ce, kamata ya yi kasashen biyu su yi aiki tare cikin kungiyoyin hadin gwiwa, ciki har da kungiyar BRICS, da kungiyar hadin gwiwa ta Shanghai(SCO) da kungiyar G20 wajen daidaita matsaloli tare da tabbatar da zaman lafiya a duniya.

Bugu da kari, shugaba Putin ya yi amfani da wannan dama wajen taya kasar Sin murnar nasarar kammala taron hadin gwiwar kasa da kasa game da shawarar " Ziri daya da hanya daya" wanda ya gudana a farkon wannan wata. Kana ya ce yana maraba da shugaba Xi Jinping na kasar Sin a ziyarar da zai kai kasar Rasha.

A nasa bangare, Wang Yi ya ce,kasashen Sin da Rasha sun amince da juna kan raya manyan tsare-tsare da fadada hadin gwiwar da ke tsakaninsu. Ya kuma yaba da kiran da shugaba Putin ya yi cewa, kamata ya yi kasashen biyu su zurfafa hadin gwiwa a fannonin kasuwanci da zuba jari kana su bullo sabbin hanyoyin bunkasa tattalin arziki.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China