in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Moscow za ta rage yawan ma'aikatan diflomasiyar Amurka dake kasar
2017-07-31 11:05:28 cri
Shugaba Vladimir Putin na kasar Rasha ya bayyana cewa, Moscow za ta rage ma'aikatan diflomasiyar Amurka 755 dake kasar, domin su yi daidai da adadin ma'aikatan diflomasiyar Rashan dake aiki a kasar ta Amurka.

Shugaba Putin wanda ya bayyana hakan yayin wata hira ta kafar talibijin din Rossiya ta kasar Rasha, ya ce, idan kasar Amurka ta rage wannan adadi, ma'aikatan diflomasiyar kowane bangare zai kasance 455 ke nan.

Ya ce, Moscow ta dauki wannan mataki ne, domin mayar da martani kan takunkumi mai tsauri da Amurkar ta kakabawa Rasha, takunkumin da shugaban Putin din ya ce ya sabawa doka.

Putin ya ce, a shirye kasarsa take ta mayar wa Amurka martani a duk lokacin da bukatar hakan ta taso, ciki har da takunkumin kan wasu sassan hadin gwiwa masu muhimmanci, wadanda ake fatan ba zai shafe su a halin yanzu ba.

A ranar Alhamis ne dai, majalisar dattawan Amurka da babban rinjaye ta amince da wani kuduri dake bukatar kakabawa Rasha takunkumi mai tsauri, kwanaki biyu bayan da kudurin ya samu amincewar majalisar dokokin kasar. (Ibrahim Yaya)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China