in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Hadin gwiwar kasashen BRICS zai gina wata sabuwar dangantakar kasa da kasa, in ji Shugaba Xi
2017-07-28 18:08:22 cri

Shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya bayyana cewa, karfafa hadin gwiwar kasashen BIRCS ba kawai zai kare tare da fadada muradun kasashen kungiyar ba, har ma zai taimaka wajen bullo da matakan gina wata sabuwar hadin gwiwar kasa da kasa.

Xi ya bayyana haka ne a Jumma'ar nan yayin da ya gana da sakataren hukumar tsaron kasar Rasha Nikolai Patrushev, da karamin ministan tsaron kasar Afirka ta kudu David Mahlobo, da mai ba da shawara kan harkokin tsaro na kasar Indiya Ajit Doval da ministan tsaron kasar Brazil Sergio Etchegoyen wadanda ke halartar taron manyan jami'an tsaron kasashen kungiyar BRICS taro na 7 a nan birnin Beijing.

Shugaba Xi ya taya murnar nasarar gudanar taron na yini biyu, inda aka tattauna batutuwan da suka shafi siyasa da harkokin tsaro tsakanin kasashe mambobin kungiyar, yana mai cewa, taron ya share fagen gudanar da taron kolin kungiyar da za a yi cikin watan Satumban wannan shekare a birnin Xiamen dake nan kasar Sin.

Mamba a majalisar zartarwar kasar Sin Mr Yang Jiechi ne ya jagoranci taron da aka gudanar tsakanin ranar Alhamis zuwa yau Jumma'a. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China