An jiyo mataimakiyar sakataren hulda da 'yan jaridu ta fadar White House Sarah Huckabee Sanders, ta ambato cikin rahoton da jaridar New York Times ta wallafa cewa, babu wani shiri game da ziyarar shugaban na Amurka zuwa kasar Birtaniya cikin wannan watan.
A cewar fadar White House, Trump zai halarci taron koli na G20 ne a birnin Hamburg na kasar Jamus tsakanin ranakun Jumma'a da Asabar, kuma zai halarci bikin muhimmiyar ranar Bastille Day a birnin Paris na kasar France a ranar 14 ga watan Yuli. Trump ya yanke shawarar soke ziyarar tasa ne zuwa kasar Birtaniya, bisa fargabar da ake yi game da yiyuwar samun mummunar zanga zanga a kasar.
Firaiministan Birtaniya Theresa May ce ta gayyaci mista Trump don ziyarar aiki a Birtaniyan tun lokacin da ta ziyarci Washington a karshen watan Janairu. (Ahmad Fagam)