Kasar Uganda da hadin gwiwar MDD ne suka jagoranci gudanarwar taron, inda suka sa ran za a samar wa kasar Uganda kudi dallar Amurka biliyan 8 cikin shekaru hudu masu zuwa, domin tunkarar matsalar samun karin 'yan gudun hijira a kasar.
Babban magatakardan MDD Antonio Guterres da shugabannin kasashen gabashin Afirka da wakilan hukumar kula da 'yan gudun hijira ta MDD da wakilan wasu hukumomin kasa da kasa da abun ya shafa, na daga cikin wadanda suka halarci taron.
Bisa kididdigar da MDD ta fitar, a halin yanzu, 'yan gudun hijira sama da miliyan 1.2 wadanda suka fito daga kasashen Sudan ta Kudu, da Congo(Kinshasa) da Burundi da kuma Ruwanda na zaune a kasar Uganda, ciki har da 'yan gudun hijirar kasar Sudan ta Kudu kimanin miliyan 1.
Wadannan 'yan gudun hijira dake zaune a kasar Uganda, na matsa wa kasar lamba kwarai da gaske, musamman ma a fannonin da suka shafi kiwon lafiya da ilmi, al'amarin da ya sa MDD da kasar ta Uganda, suka bukaci gamayyar kasa da kasa da su samar da taimakon kudi don sassauta matsalar. (Maryam)