in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Uganda tana son kara hadin gwiwa a tsakaninta da Sin a fannin bada ilmi
2017-05-31 13:34:20 cri
Ministan harkokin ilmi na kasar Uganda John Chrysostom Muyingo ya bayyana cewa, an samu nasarori da dama kan hadin gwiwar bada ilmi a tsakanin Uganda da Sin, kuma yana fatan za a ci gaba da kara irin wannan hadin gwiwar a nan gaba.

A wannan rana, an gudanar da bikin ban kwana ga daliban da suka samu damar shiga shirin samar da iri domin amfanin nan gaba, wato Seeds for the Future karo na biyu na kamfanin Huawei dake kasar Uganda a jami'ar Makerere ta kasar Uganda. Minista Muyingo ya bayyana cewa, yana fatan za a kara yin hadin gwiwar bada ilmi tare da kasar Sin, musamman fadada hadin gwiwa da yin mu'amala tare da hukumomi masu zaman kansu, da sa kaimi ga dalibai da malamai na kasar Sin da su zo Uganda don kai ziyara da yin karatu.

Jakadan Sin dake kasar Uganda Zheng Zhuqiang ya bayyana a gun bikin cewa, Sin za ta ci gaba da zurfafa hadin gwiwar sada zumunta a tsakaninta da Uganda, tare da fatan shirin Seeds for the Future zai zama abu mai sa kaimi ga sada zumunta a tsakanin kasashen biyu.

Mukaddashin mataimakin shugaban jami'ar Makerere Ernest Okello Ogwang ya bayyana cewa, shirin Seeds for the Future ya samar da yanayin sanin al'adu daban daban, yana fatan jami'o'in kasar Uganda za su rike wannan dama don daga karfin nazarin kimiyya da fasaha. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China