Da yake jawabi ga mahalarta taron, mataimakin babban sakataren kungiyar kasashen Larabawa mai kula da harkokin siyasar kasa da kasa Khalid al-Habas, ya ce manufar shirya wannan taro ita ce karfafa hadin gwiwa da tuntubar juna tsakanin sassan biyu, ganin yadda sassan ke da tsarin al'adu da bayanan tarihi iri daya.
A nata jawabin kwamishinar kungiyar tarayyar Afirka mai kula da harkokin jin dadin jama'a Amira al-Fadil, ta jaddada muhimmancin halartar tawagar kungiyar mai kunshe da kwararru a fannonin daban daban, wadanda ake fatan za su tattauna a wannan taro.
Ana fatan taron zai ba da shawarwari game da taron hadin gwiwar shugabannin kungiyoyin biyu da aka shirya gudanarwa a karshen wannan shekara ta 2017. (Ibrahim Yaya)