in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An bude taron koli karo na 29 na kungiyar tarayyar Afirka
2017-07-03 19:20:38 cri

A yau Litinin 3 ga watan nan ne aka bude taron koli karo na 29 na kungiyar tarayyar Afirka ta AU, taron da ke gudana a kasar Habasha.

A wannan karo dai taron na da taken "cin gajiyar banbance banbance dake tsakanin kasashe ta hanyar zuba jari kan matasa", kaza lika shugabannin kasashe mambobin kungiyar za su yi amfani da wannan dama, wajen tattaunawa kan harkokin samar da sauye sauye a bangaren tattara kudade, da inganta tsarin gudanarwa a nahiyar. Kaza lika za su nazarci batutuwan tsaro da wanzar da zaman lafiya a sassan nahiyar ta Afirka.

Taron na yini biyu, shi ne na farko da AU ta shirya, tun bayan zaben sabbin jami'an hukumar zartaswar kungiyar, inda aka zabi Moussa Faki Mohamat a matsayin sabon jagoran ta.(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China