in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An kammala taron kolin kuingiyar AU
2017-07-05 09:52:15 cri
A jiya ne aka kammala taron kolin kungiyar tarayyar Afirka (AU) karo na 29 a birnin Addis Ababa na kasar Habasha, tare da yin kira ga shugabannin kasashen nahiyar da su kara hada kai don manyan matsalolin dake addabar kasa da kasa da shiyya-shiyya.

A jawabinsa na rufe taron, shugaban kungiyar, kana shugaban kasar Jamhuriyar Guinea Alpha Conde ya yi kira ga shugabannin kasashen Afirka da su rika magana da murya guda, kana su kara hada kai don magance matsalar tsaro da zaman lafiya, da yadda matasa ke kaura daga nahiyar don neman rayuwa mai kyau da sauran muhimman batutuwa da nahiyar ke fama da su.

Sauran batutuwan da taron kolin ya tabo sun hada da batun aiwatar da gyare-gyare a cikin kungiyar da yadda za a inganta rayuwar matasan nahiyar.

Shi ma shugaban hukumar zartarwar kungiyar Moussa Faki Mahamat ya ce, taron kolin ya tabo batun yadda kungiyar za ta rika samun kudaden tafiyar da harkokinta don rage dogara kan abubuwan hulda, da batun tashe-tashen hankulan dake faruwa a kasashen Sudan ta kudu, yankin Sahel, da tafkin Chadi da yankin Afirka ta tsakiya.

Har ila a yayin rufe taron kolin kungiyar ce aka rantsar da dan kasar Madagascar a matsayin kwamishinan kungiyar mai kula da harkokin tattalin arziki, sai kuma dan kasar Kamaru da aka nada a matsayin kwamishinan kungiyar ta AU mai kula da albarkatun jama'a, kimiya da fasahar kere-kere. (Ibrahim Yaya)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China