in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
AU ta musanta rahoton dake cewa Al-Shabaab ta hallaka sojoji 39
2017-07-31 10:23:40 cri
Tawagar wanzar da zaman lafiya ta kungiyar tarayyar Afrika dake aiki a kasar Somalia (AMISOM) ta karyata rahotannin dake cewa Al-Shabaab ta hallaka sojoji 39 a kudancin Somalia.

Da yake zantawa da manema labarai a Mogadishu, mai magana da yawun AMISOM Joe Kibet, ya tabbatar da cewa an kaddamar da harin amma ya musanta hallaka ko da soja guda a gundumar Bulaamareer dake yankin Lower Shabelle.

Ya ce sabanin rahotannin da kafafen yada labarai suka watsa inda suka danganta abin da mai magana da yawun Al-Shabaab Abdiasis Abu Musab wanda ya ce an kashe sojoji 39, ya ce adadin sojojin kasar dake cikin tagawar ba su ma kai yawan abin da aka yi ikirarin kashewa ba.

Kibet ya bayyana cewa yawancin bataliya guda ba ta wuce adadin sojoji 39.

Rahotannin da kafafen yada labarai suka watsa da wasu shafukan intanet suka wallafa ya nuna cewa Al-Shabaab ta yi ikirarin hallaka sojojin AMISOM 39 daga Uganda inda ta hallaka su saboda girman makamansu. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China