in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
'Yan asalin Afrika sama da 5,000 ne suka shiga kungiyoyin ta'addanci na duniya
2017-07-04 10:52:41 cri
Wasu takardun bayanai sun nuna cewa 'yan asalin kasashen Afrika sama da 5,000 ne suka shiga kungiyoyin 'yan ta'adda na duniya baki daya, musamman a kasashen Iraki, Sham da yankin Sahel na Afrika.

Kamfanin dillancin labarai na APS ya rawaito cewa, firaiministan kasar Algeriya Abdelmadjid Teboune, shi ne ya gabatar da takardun bayanan a ranar Litinin a lokacin taron koli na AU karo 29 a Addis Ababa.

Shugaban kasar Algeriya Abdelaziz Bouteflika, ya tsawaita takardun bayanan inda ya tabo batun irin matakai da suka dace kungiyar tarayyar Afrika ta dauka domin yin rigakafin matsalolin tashe tashen hankula na masu tsattsauran ra'ayi da kuma hanyoyin yaki da ta'addanci.

ASP ya ruwaito cikin wannan taftari cewa, da yawa daga cikin matasan Afrika sun tsunduma cikin ayyukan ta'addanci a sassa daban daban na duniya, musamman a kasashen Iraki, Sham da yankin Sahel na Afrika. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China