in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Babban hafsan sojojin kasa na Najeriya ya bukaci dakarun kasar da su kara sanya-ido
2017-08-03 09:19:37 cri
Babban hafsan mayakan kasa na Najeriya Laftana-janar Tukur Buratai ya bukaci dakarun kasar da ke fafatawa da mayakan Boko Haram a yankin arewa maso gabashin kasar da su kasance cikin shirin kota-kwana.

Janar Buratai wanda ya yi wannan kiran a jiya Laraba yayin da ke yiwa dakarun bataliya ta uku dake garin Damaturu, babban birnin jihar Yobe jawabi, ya ce akwai jan aiki a gaban dakarun a kokarin da ke na kakkabe gyauron 'yan ta'addan Boko Haram. Babban haftan sojojin ya ce har yanzu 'yan ta'addan na haifar da barazana a wasu yankunan shiyyar, inda suke kai hare-hare tare da sace mutane don neman kudin fansa.

A halin da ake ciki kuma, rundunar sojojin Najeriyar ta yi kira ga jama'a da su taimakawa sojojinta da muhimman bayanai ta yadda za su yi nasara a yakin da suke yi da masu tayar da kayar baya.

Shi ma kakakin hukumar tsaron kasar Manjo Janar John Eneche kira ya yi ga 'yan Najeriya da su rika taimakawa sojojin kasar da muhimman bayanan da su taimaka wajen kawo karshen ayyukan mayakan Boko Haram a yankin arewa maso gabashin kasar cikin hanzari. (Ibrahim Yaya)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China