in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Najeriya za ta tura dakarun wanzar da zaman lafiya sama da 200 zuwa kasar Liberiya
2017-07-30 09:52:32 cri
Najeriya ta bayyana cewa za ta tura dakarun wanzar da zaman lafiya kimanin 230 zuwa kasar Liberiya cikinsu har da manyan hafsoshi 19.

Babban hafsan sojojin kasar Tukur Buratai ya ce dakarun sojin da za'a tura za su yi aiki ne karkashin tawagar wanzar da tsaro ta MDD dake Liberiyar wato UNMIL.

Da yake jawabi a lokacin wani shirin bada horo na musamman na tsawon makonni 4, wanda aka shiryawa sojojin a Kaduna, dake arewa maso yammacin kasar, Buratai ya gargadi sojojin da su guji aikata duk wani abu da ka iya zubar da kimar Najeriyar.

Kana ya hore su da su mutunta hakkin bil adama, kuma su girmama al'adu da addinai na al'ummar kasar ta Liberiya. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China