Da yake karin haske kan hakan, Sani Kukasheka Usman, kakakin rundunar sojojin Najeriyar, ya ce gawawwakin da aka gano sun hada da na sojoji biyar wadanda ke yiwa tawagar ma'aikatan rakiya, da 'yan kato da gora 11 sai kuma na ma'aikatan kamfanin mai na kasar wato NNPC guda biyar. Sai dai har yanzu akwai ragowar ma'aikatan kamfanin mai na NNPC guda 6 daga cikin 12 dake aiki a cikin tawagar da ba a ji duriyarsu ba, baya ga mutum guda da ya dawo sansanin tawagar da ransa. Ana ci gaba da gudanar da bincike don gano ma'aikatan da ransu.
A ranar Alhamis din da ta gabata ce, dai mahukuntan Najeriyar suka sanar da dakatar da aikin hako mai a yankin na tafkin Chadi sakamakon harin da ake zargin kungiyar Boko Haram da kaiwa tawagar ma'aikatan dake aikin hako mai a yankin Magumeri na jihar Borno dake yankin arewa maso gabashin kasar ta Najeriya. (Ibrahim Yaya)