Baya ga dimbin alfanun da shayarwa ke da shi, kasar dake yammacin Afrika na da burin inganta tsarin shayar da nonon uwa zalla, yadda zai yi daidai da matsakaicin mataki na duniya da a kalla kashi 50 cikin dari zuwa shekarar 2025.
An kaddamar da shirin mai taken 'wayar da kai game da shayarwa' a jiya Talata, a daidai lokacin da aka shiga makon shayarwa na duniya mai taken 'shayarwa a tare mai dorewa'
A cewar Ministan Lafiya na kasar, kimanin kashi 25 cikin dari na iyaye ne kadai suka san cewa, dole ne a shayar da yara nonon uwa zalla cikin farkon watanni 6 da haihuwa.
Ita kuwa shugabar sashen kula da abinci da sinadaran gina jikin yara ta ma'aikatar, Grace Mojekwu, cewa ta yi, nonon uwa shi ne abinci mafi dacewa ga jariri.
Grace Mjekwu ta kara da cewa, baya ga rage mace-mace jarirai, an yi imanin nonon uwa na taimakawa wajen wasan kwakwalwar yara, domin yaran da aka shayar da su, suna kokari a makaranta, sannann ana alakanta kaifin basira da shayarwa na tsawon lokaci.
Ta ce za su matse kaimi wajen wayar da kai game da shayar da nonon uwa zalla da dabi'ar ciyar da yara a asibitoci da cikin al'umma da wuraren aiki tare kuma da kara horar da jami'an kiwon lafiya. (Fa'iza Mustapha)