in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mutane 14 ne suka mutu a tagwayen harin bam a Najeriya
2017-07-31 09:54:33 cri
Adadin mutanen da suka mutu a sanadiyyar harin tagwayen bama bamai a sansanin 'yan gudun hijira a jihar Borno dake arewa maso gabashin Najeriya ya kai mutane 14, hukumar bada agajin gaggawa ne ta bayyana a hakan a ranar Lahadi.

Hukumar agajin gaggawa ta jihar Borno ta shedawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa mutane 15 ne suka jikkata a sanadiyyar harin kunar bakin waken.

Rawa Modu, shugaban karamar hukumar Dikwa dake jahar Borno ya bayyana cewa, wasu mata biyu 'yan kunar bakin wake ne suka tada boma boman da yammacin ranar Jumma'ar da ta gabata.

Modu ya ce maharan sun kutsa ne cikin sansanin 'yan gudun hijirar inda suka tada boma boman dake jikinsu.

Mahukunta sun bayyana cewa, mutane 7 ne suka mutu nan take a wajen da aka kaddamar da harin, yayin da ragowar mutanen suka mutu a asibiti.

Ana zargin kungiyar Boko Haram da alhakin kaddamar da harin. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China