in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Lucas Lima na Brazil zai koma Barcelona
2017-06-28 16:05:13 cri
Dan wasan tsakiya na kungiyar wasan Brazil Lucas Lima ya amince zai koma kungiyar wasa ta Barcelona bisa tsarin musaya a watan Janairu, kamar yadda rahotannin kafafen yada labarai suka rawaito.

Dan wasan mai shekaru 26 a duniya yana da ragowar watanni 6 na kwantiragin da ya kulla da kulob din Brazilian Serie A club Santos, hakan na nufin zai iya sanya hannu kan kwantiragin ta wucin gadi da Catalan giants a wata mai zuwa.

Zai iya samun albashi da yakai euro miliyan 4 a duk shekara, ciki har da garabasar euro miliyan 5, kamar yadda jaridar Globo ta rawaito.

Lima ya sake samun wani tayin wasa daga kungiyoyin wasan na Everton da Fenerbahce na kasar Turkiyya a gasar wasanni Premier.

Santos ta tabbatar da labarin cewa Bruno Henrique abokan wasansa sun tafi a tun a ranar Alhamis.

Henrique ya shedawa yan jaridu cewa suna tayashi murna, saboda irin salon wasan da yake bugawa. Yace yana da kwarewa, kuma ingancin da yake dashi ba abu ne da za'a yi tababa kansa ba, dan wasan kasa da kasa na Brazil. Ya taimakawa Santos. Ana yi masa fatan alheri mai yawa na komawarsa Barcelona.

Lima ya bayyana sau 95 tun a lokacin komwarsa Santos wasa daga kungiyar wasan Sport Recife a 2014. Yayi nasarar samawa Brazil nasarori har sau 14.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China