in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Angola ta lallasa Sin a wasan kwallon kwando na kwararru na 2017
2017-08-02 17:46:09 cri
Angola ta doke kungiyar wasan kwallon kwando ta Blue Team ta kasar Sin da ci 73-65 a zagaye na biyu a wasan kwallon kwandon na Kunshan na 2017.

Carlos Morais shine ya samarwa kungiyar wasan ta Angola maki 6 daga cikin adadin maki 8, lamarin da ya baiwa kungiyar wasan ta Angola tazarar maki 2 inda ta samu maki mafi yawa wanda yakai maki 20, Reggie Moore da Yanick Moreira dukkanninsu sun samu maki 15 kowannensu. Dan wasan kasar Sin Zhou Peng ya bada gudunmowar maki 19 da Guo Ailun ya samu maki 13 da kuma maki 7.

Du Feng, babban kociyan kungiyar wasan ta Team Blue yace "yan wasanmu suna da karanci sha'awar wasan sakamakon gajiya; na lura da hakan ne a lokacin motsa jiki. Mun rasa buga wasannin masu yawa da bugun kai tsaye, kuma sun yi mana fintinkau da ci 40-31".

China ta samu maki 3 ne kacal daga cikin maki 17 maki 3 kacal ta samu a yunkurin data yi yayin da Angola ta binne China da maki 11 a wasan.

Bayan kungiyoyin biyu sun fafata a zagayen farko, Angola ta samu bugu 11-1 inda ta zamanto a kan gaba da 32-23, amma Han Dejun ya samu maki 2 da 3 inda ya taimakawa Sin ta cike gibin zuwa 32-36 kafin zuwa hutun rabin lokaci. Daga nan Morais ya karbe wasan, inda ya samu maki 3 wanda ya baiwa Angola samun nasara mafi girma ta maki 45-33 a zagayen karshe.

Angola ce ke kan gaba da maki 56-47 bayan zagaye na uku na wasan. Sin ta samu maki 35 a matsayi na biyu a wasan, amma Moreira ya samu nasara ne bayan da ya kasance wanda ya lashe wasan da maki 3.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China