A shekaru biyu da suka gabata, a gasar wasan kwallon kwando ta nahiyar Turai da ya gabata, kungiyar kasar Spaniya ce ta zo matsayi na uku. Koda yake kungiyar kasar Spaniya ta fuskanci wasu matsaloli a wasan ta farko da na biyu a gasar a wannan karo, amma hakan bai hana ta doke kungiyoyi da suka kara da ita a gasar ba wadda daga karshe ta zama zakara. Wannan ne karo na uku da kungiyar kasar Spaniya ta zama zakara a dukkan gasannin 4 na kwallon kwando na nahiyar Turai. Ga kungiyar kasar Lithuania, wannan ne karo na biyu da ta zo matsayi na biyu a gasar, a wannan karo da kuma gasar shekarar 2013 inda Faransa ta doke ta.
Paul Gasol dan wasan kungiyar wasan kwallon kwando ta kasar Spaniya ya bayyana cewa, dukkan 'yan wasan kungiyar sun yi farin ciki sosai da da wannan nasara da suka samu a wannan karo.
Cikin wadanda suka kalli gasar karshe,sun hada da sarkin kasar Spaniya Felipe VI da fitaccen dan wasan tennis dan kasar Spaniya Rafael Nadal, kuma kungiyar kasar Spaniya ta doke kasar Lithuania ba tare da wata wahala ba.
A karshen gasar, Paul Gasol ya samu lambar yabo ta dan wasa mafi kwazo a gasar ta wannan karo. Ita kuma kasar Faransa ta doke kasar Serbia lamarin da ya ba ta damar kasancewa a matsayi na uku a gasar.
Bisa wannan sakamko, kasashen Spaniya da Lithuania za su shiga gasar wasannin Olympics da za a yi a Rio a shekarar 2016 kai tsaye. Kungiyoyin da suka kasance daga matsayi na uku zuwa na bakwai za su shiga wasannin shiga gasar wasannin Olympics na gaba. (Zainab)