Gumisiriza ya ce suna sa ran isar Temitope kungiyar nan gaba kada, matakin da zai taimakawa 'yan wasan ta samun karin gogewa, daga irin kwarewar da dan wasan ke da ita, musamman a gabar da kulaf din ke fatan daukar kofin gasar zakarun kasar na bana.
A nasa bangare Temitope, wanda a baya ya bugawa kungiyoyin kasashen Indonesia, da Thailand da Malaysia wasa, ya alkawarta baiwa sabuwar kungiyar ta sa cikakkiyar gudummawar da ta dace.
A wani ci gaban kuma, kungiyar mata ta kwallon Kwando a Najeriya na shirin shiga jerin 'yan wasan kasashe daban daban, wanda za su buga gasar Olympics ta birnin Rio. Yanzu dai haka kungiyar mai suna Tigress za ta buga wasannin share fagen gasar ta Rio da za a buga a kasar Faransa, tsakanin ranekun 13 zuwa 19 ga watan Yuni mai zuwa.
Kungiyar 'yan matan dai na cikin rukuni na C, za kuma ta fafata da kasashen Koriya ta kudu, da Belarus a birnin Nantes na kasar ta Faransa.
Da take karin haske game da shirin kungiyar Helen Ogunjimi, ta ce 'yan wasan na Najeriya za su yi duk mai yiwuwa, wajen samun gurbi a gasar ta Olympics.
Ita ma Sarah Ogoke, wadda daya ce daga taurarin 'yan wasan na Najeriya, ta ce za su yi iyakacin kokarin samarwa Najeriya nasara, a wasannin share fage da kuma gasar ta birnin Rio.(Saminu Alhassan)