Bisa shirin da kasar Sin ta gabatar, birane 8 na wato Beijing, da Nanjing, da Suzhou, da Wuhan, da Guangzhou, da Foushan, da Shenzhen da Dongwan ne za a gudanar da wasannin gasar a cikin su.
Kasar Sin da kasar Philippines ne suka yi takara a zaben neman daukar bakuncin gasar cin kofin duniyar ta kwallon kwando a wannan karo, kana mambobin kwamitin hukumar ta FIBA su 24 daga kasashe daban daban suka jefa kuri'un da suka tabbatarwa Sin din wannan dama.
An dai canja sunan gasar wasan kwallon kwando ta duniya, zuwa gasar cin kofin duniya ta kwallon kwado, wadda kuma gasar ta 2019 za ta kasance ta 2 bayan sauyin sunan da aka yi.
Bisa tarihi an gudanar da gasar cin kofin duniya ta kwallon kwando karo na farko ne a kasar Spaniya, inda kasar Amurka ta cimma nasarar lashe wannan gasa, kuma kasar Sin ba ta shiga gasar a wancan lokaci ba. An ce, za a kara yawan kungiyoyin da za su halarci gasar cin kofin duniya ta kwallon kwando karo na biyu a shekarar 2019, daga kungiyoyi 24 a karon da ya gabata zuwa 32 a wannan karo. (Zainab)