in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kwamishinan hukumar NBA yayi tsokaci game da fadada wuraren gudanar All-Star game
2016-02-17 09:17:04 cri
Kwamishinan hukumar NBA Adam Silver, yayi tsokaci game da fadada wuraren gudanar da gasar duniya, ta kwallon Kwando ajin kwararru ta All-Star wadda NBA ke shiryawa.

Yayin wani biki da NBA ta shirya a karshen mako a birnin Toronto na kasar Canada, Silver ya yi karin haske ga wakilin kamfanin dillancin labaran kasar Sin, game da muhimman batutuwa da suka shafi kwallon Kwando, ciki hadda yiwuwar shirya gasar All-Star game a wajen kasar Amurka a nan gaba

Wannan ne dai karo na farko cikin shekaru 65 da NBA ta shirya liyafar ta ta shekara a wata kasa wajen Amurka.

Game da yiwuwar gudanar gasar ta All-Star Game a wani yanki na daban, Silver ya ce har yanzu basu tsallaka teku da gasar ba tukuna, amma idan har damar hakan ta bijiru, mai yiwuwa ne su leka da gasar nahiyar Turai saboda kusancin ta da nahiyar Arewacin Amurka.

Ya ce baya ga Amurka da Canada, yanki na gaba da NBA ka iya kai gasar ta All-Star Game shi ne nahiyar Asiya. Kwamishinan nan NBA ya kara da cewa yanzu haka hukumar ta gudanar da wasannin kasa da kasa 158, da suka hada da gasannin kakar wasanni 20, don haka fidda babbar gasar da hukumar ke shiryawa zuwa wasu sassan duniya, na cikin muhimman burukan ta a nan gaba.

Game da tasirin da shahararren dan wasan kwallon kwando Kobe Bryant ke yi ga ci gaban wasan kwallon Kwando a yanzu haka kuwa, Silver ya ce shi da Bryant sun halarci gasar Olympics ta shekarar 2008 da ta gudana a birnin Beijing, ya kuma yi mamakin yadda dan wasan ya samu karbuwa daga masoyansa.

Yace Bryant ya halarci wasanni da dama, ya kuma gana da wakilan kamfanonin kasar Sin, da masu goyon bayan sa masu yawa a yayin gasar Olympics ta birnin Beijing. Yanzu haka dai Bryant mai shekaru 37 da haihuwa, wanda kuma ya lashe lambar karramawa ta gwarzon dan wasan hukumar ta NBA har karo 18, ya bayyana aniyar sa ta sallama da gasar NBA tun daga kakar wasanni ta wannan karo.

A daya bangaren kuma Silver ya ce sun yi farin cikin halartar Yao Ming bikin na bana, duk da kasancewar bikin ya gudana a lokacin da Sinawa ke shagulgulan bikin bazara na wannan shekara.

Ya ce a watan Oktobar da ta gabata ya ziyarci kasar Sin, inda a lokacin ne ya gabatarwa Yao Ming bukatar halartar bikin na kasar Canada, nan take kuma ya amsa gayyatar. Yao Ming dan asalin kasar Sin dai na cikin shahararrun 'yan wasan kwallon Kwando na duniya, wanda kuma ke da matukar farin jini a harkar wasan kwallon Kwando.(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China