in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An dakatar da kungiyar kwallon kwando ta kasar Brazil daga shiga gasannin kasa da kasa
2016-11-16 15:55:34 cri
Hukumar kula da kwallon Kwando ta kasa da kasa FIBA, ta ce ta dakatar da kasar Brazil daga shiga gasannin kasa da kasa, bayan da aka samu hukumar kwallon kwandon kasar CBB, da laifin karya manyan dokokin da suka shafi wasan.

Cikin wata sanarwa da FIBA ta fitar a ranar Litinin, ta ce hukumar kwallon Kwando ta kasar Brazil CBB, ta gaza tura 'yan wasan ta na ajin matasa, da na babbar kungiyar kasar zuwa gasannin da ya dace su halarta. Kaza lika kasar ta soke gasar da aka shirya gudanarwa a birnin Rio de Janeiro, wanda hakan ya sabawa ka'idojin hukumar.

Har wa yau FIBA ta zargi hukumar CBB da shiga harkokin da ba na ta ba ta fuskar sarrafa kudade da tsara wasanni, baya ga sakaci wajen kyale wasu da ba masu ruwa da tsaki ba, su shiga sabgar zabar 'yan wasan kwallon kwandon kasar cikin wani yanayi dake nuni da yiwuwar aikata almundahana. Bugu da kari FIBA ta ce tana bin CBB bashin wasu kudade.

Hukumar FIBA mai helkwata a kasar Switzerland ta ce za ta sake nazartar wannan mataki da ta dauka, yayin taron ta na watan Janairun sabuwar shekara mai zuwa.

Sai dai a hannu guda hukumar CBB ta Brazil, ta ce tayi mamakin wannan mataki da aka dauka a kanta, kuma za bi hanyoyin shari'a mafiya dacewa domin bin bahasin hakkin ta.(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China