in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Firaministocin Sin da Indiya sun gana da manema labaru a nan Beijing
2015-05-15 18:19:41 cri

A yau Jumma'a da safe ne, firaministan kasar Sin Li Keqiang da takawaransa na kasar Indiya Narendra Modi suka gana da manema labaru a nan birnin Beijing, hedkwatar kasar Sin.

Mista Li ya ce, shi da mista Modi da yin shawarwarin sada zumunta yadda ya kamata, inda suka cimma daidaito kan yadda za su kara inganta amincewa da juna, zurfafa hadin gwiwar da ta dace a sassa daban daban, da kara raya dankon huldar bunkasuwa da abokantaka a tsakanin kasashen 2.

Jami'an biyu na ganin cewa, moriyar bai daya a tsakanin Sin da Indiya ta fi sabanin da ke tsakaninsu. Kasar Sin na son hada kai da Indiya wajen yin amfani da zarafi da kawar da sabani, a kokarin raya huldar da ke tsakaninsu zuwa sabon mataki, da kuma taka rawa wajen samun kwanciyar hankali da wadata a shiyyar da suke ciki da ma duniya baki daya.

A nasa bangaren, mista Modi ya ce, a yayin ziyararsa a nan kasar Sin, ya yi mu'amalar sada zumunta tare da shugabannin Sin ba tare da wata rufa-rufa ba, inda suka cimma ra'ayi daya a wasu muhimman fannoni da kuma tabbatar da muhimmiyar alkiblar da ta kamata a kalla.

Ya ce, kasarsa na son yin kokari tare da kasar Sin a fannonin yin mu'amala a tsakanin manyan jami'ai, daidaita sabanin da ke tsakanin kasashen 2, zurfafa hadin gwiwarsu, habaka mu'amalar al'adu, inganta tuntubar juna a al'amuran shiyya-shiyya da na kasa da kasa, a kokarin kara azama kan samun zaman lafiya da bunkasuwa a shiyyar da kasashen 2 suke ciki da ma duniya baki daya. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China