Bayan aukuwar hare-haren, hukumar lafiya ta kasar ta tabbatar da cewa, hare-haren sun haddasa mutuwar mutane 16, tare da jikkata wasu 59, ciki har da yara da mata.
Bayan aukuwar lamarin, kungiyar Taliban ta sanar da daukar alhakin hare-haren.
Cikin kakkausar murya, shugaban kasar Ashraf Ghani ya yi allah wadai da wadananan hare-hare.
A 'yan kwanakin nan, damuwa ta yi tsanani game da yanayin tsaro a kasar Afghanistan, duk da cewa, dakarun kasar sun karfafa yaki da suke kai da 'yan adawa, har yanzu masu adawar da na ci gaba da kai hare-hare. (Maryam)