Za a gudanar da taron wakilan kula da harkokin tsaron kasashen BRICS karo na 7 a birnin Beijing
Za a gudanar da taron wakilan kula da harkokin tsaron kasashen BRICS karo na 7 a birnin Beijing tun daga ranar 27 zuwa 28 ga wannan wata. Wannan taro yana daya daga cikin tarurukan da za a gudanar tun lokacin da kasar Sin ta karbi shugabancin kungiyar BRICS a wannan karo a bana. A kuma saran mamban majalisar gudanarwar kasar Sin Yang Jiechi ne zai shugabanci taron.
Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Lu Kang ya bayyana yayin taron manema labaru da aka gudanar a yau cewa, kasar Sin tana fatan za a kara tabbatar da moriyar juna da sa kaimi ga inganta hadin gwiwa a tsakanin kasashen BRICS a fannin tsaron siyasa, da inganta hadin gwiwarsu ta hanyar gudanar da wannan taro. Daga bisani kuma za a shirya ganawar shugabannin kasashen BRICS da za a gudanar a birnin Xiamen a watan Satumba na bana. (Zainab)