Bikin dai ya samu halartar manyan jami'an gwamnatocin kasashen biyu, ciki har da ministan kula da ayyukan gine-gine na Aljeriya Abdelmadjid Teboune, da gwamnan Algiers Abdelkader Zoukh, tare kuma da jakadan Sin dake Aljeriyar Mista Yang Guanyu.
Minista Abdelmadjid Teboune ya bayyana cewa, wannan babban aiki ya kara shaida irin kyakkyawar dangantaka dake tsakanin Sin da Aljeriya, inda ya mika godiyar kasarsa ga kasar Sin, saboda wannan katafaren aikin da ta yi, wanda zai zama abun tarihi, kana masallaci mafi girma na uku a duniya, bayan masallatai biyu na biranen Makka da Madina a kasar Saudiyya.
Rahotanni sun ce, za a kammala aikin gina wannan masallaci na Aljeriya ne a watan Disambar bana, wanda a lokacin fadinsa zai kai murabba'in mita dubu dari hudu.(Murtala Zhang)