in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mataimakin shugaban kasar Ghana ya nemi 'yan kasuwar kasar Sudan su zuba jari a Ghana
2017-07-11 10:58:29 cri
Mataimakin shugaban kasar Ghana Muhammadu Bawumia, ya bukaci 'yan kasuwar Sudan su zuba hannayen jari a kasar Ghanan, kana ya kalubalanci 'yan kasuwar Ghanan da su karfafa kyakkyawar dangantaka da takwarorinsu na kasar Sudan.

Ya bayyana cewa akwai damammakin kasuwanci masu yawa a kasar ta Ghana, ya nanata cewa babban abin da gwamnatin shugaban kasar Akufo-Addo ta fi bada fifiko shi ne mayar da kasar ta yammacin Afrika don ta zama babbar aminiya ta fuskar huldar kasuwanci a tsakanin dukkan kasashen nahiyar ta Afrika.

Bawumia yana jawabi ne a lokacin da ya karbi bakuncin karamin ministan zuba jari na kasar Sudan Osama Faisal Elsayed Ali, wanda ya kai ziyara a fadar mulkin kasar dake birnin Accra.

Mataimakin shugaban kasar ta Ghana ya ja hankalin masu zuba jari 'yan asalin kasar Ghanan da su yi amfani da kyakkyawar dangantakar dake tsakanin kasashen biyu wajen zuba jari mai dimbin yawa a kasar domin samar da babbar moriya.

Ya bayyana cewa wannan hadin gwiwar za ta samar da damammaki wajen karfafa kyakkyawar dangantakar siyasa da ta diplomasiyya tsakanin kasar Sudan da Ghana.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China