in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Xi Jinping: ya kamata a inganta karfin sojoji ta yadda zai dace da yanayin kasar Sin
2017-08-01 11:32:03 cri

A yau 1 ga watan Agusta a babban dakin taron jama'a dake nan birnin Beijing, aka gudanar da taron murnar cika shekaru 90 da kafuwar sojojin 'yantar da jama'ar kasar Sin PLA, inda babban sakataren kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta Sin kuma shugaban kasar Sin kana shugaban kwamitin tsakiya mai kula da harkokin sojan kasar, Xi Jinping ya halarci taron tare da yin wani muhimmin jawabi.

Xi Jinping ya jaddada cewa, muddin ana bukatar samarwa al'ummar Sinawa ci gaba gami da rayuwa mai inganci, tilas ne a raya sojojin jama'ar kasar a matsayin sojoji da suka fi karfi a duniya, ya kamata a ci gaba da martaba manufofi da aka tsara tun farko da samun bunkasuwa, da daukar matakan inganta karfin sojoji da yadda zai dace da yanayin kasar Sin, da kuma sa kaimi ga inganta karfin sojojin kasar yadda ya kamata. (Zainab Zhang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China