in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Taron CPC na 19 dake tafe wani muhimman lokaci ne da ake kokarin gina tsarin gurguzu na musamman mai sigar kasar Sin, in ji shugaba Xi
2017-07-27 20:16:58 cri

Shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya bayyana cewa, tun lokacin da aka kammala taron wakilan Jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin CPC karo na 18 shekaru biyar da suka gabata, majalisar ke kara zage damtse a kokarin ganin an aiwatar da matakan da suka shafi jam'iyyar da ma kasar baki daya.

Shugaba Xi wanda ya bayyana hakan yayin taron karawa juna sani na manyan jami'ai gabanin taron CPC karo na 19, ya ce kasar Sin za ta ci gaba da aiwatar da matakan zurfafa yin gyare-gyare a fannin samar da kayayyaki domin samun ci gaban tattalin arziki mai dorewa da inganta rayuwar jama'a. Kana yaki cin hanci da rashawa da gwamnati take yi ya cimma nasara.

Bugu da kari, shugaba Xi ya ce taron CPC dake tafe wani muhimmin taro ne a wani muhimmin lokaci da ake kokarin gina tsarin gurguzu na musamman mai sigar kasar Sin.

Shugaba Xi ya jaddada bukatar a kara daura damara don yin rigakafi tare da hana fadawa manyan matsaloli, da rage talauci da kuma kiyaye gurbatar muhalli. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China