in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Sin ya yi kira da a nacewa manufofin JKS
2017-07-28 09:36:08 cri

Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya ja hankalin wakilan JKS, da su kara azama wajen martaba manufofin jam'iyyar, tare da tabbatar da karfafa jagorancin ta, ta yadda za ta ci gaba da kasancewa jigo ga cimma burin ciyar da kasa gaba.

Shugaba Xi wanda shi ne kuma babban sakataren jam'iyyar, ya yi wannan kira ne, yayin wani taron karawa juna sani da aka shirya, gabanin babban taron jam'iyyar karo na 19 dake tafe.

Ya ce, gina jam'iyya mai nagarta, zai taimaka wajen cimma nasarar jogoranci na gari, ya kuma ba da damar shawo kan dukkanin kalubale da kasar Sin ke fuskanta, da ma duk wata barazana ko wani shinge daka iya takawa nasarar kasar birki.

Shugaban na Sin ya jinjinawa nasarar da JKS ta cimma, tun bayan babban taron ta na 18, sai dai kuma ya ce, ya zama wajibi a kaucewa sakaci ko ci-da-zuci, duba da cewa, har yanzu akwai tarin kalubale gaban jam'iyyar.

Taron karawa juna sanin na ranekun Laraba da Alhamis dai ya samu halartar manyan jami'an larduna da na gwamnatin tsakiyar kasar Sin.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China