in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An gudanar da taron murnar cika shekaru 90 da kafuwar PLA
2017-08-01 10:12:41 cri

A yau 1 ga watan Agusta a babban dakin taron jama'a dake nan birnin Beijing, aka gudanar da taron murnar cika shekaru 90 da kafuwar sojojin 'yantar da jama'ar kasar Sin PLA, inda babban sakataren kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta Sin kuma shugaban kasar Sin kana shugaban kwamitin tsakiya mai kula da harkokin sojan kasar, Xi Jinping ya halarci taron tare da yin wani muhimmin jawabi.

Taron ya kuma samu halartar dukkan zaunannen membobi 7 na hukumar siyasa na kwamitin tsakiyar jam'iyyar kwaminis ta Sin, da shugabannin kasa da na jam'iyyar kwaminis ta Sin wadanda suke nan birnin Beijing, da kuma wakilai daga bangarori daban daban kimanin 3000.  (Zainab Zhang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China