in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Xi Jinping: Sin na goyon bayan kafa kasashe biyu domin warware rikicin Palasdinu
2017-07-18 20:24:40 cri
Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya ce kasar sa na goyon bayan warware rikicin siyasar Palasdinu da Israila ta hanyar siyasa, musamman wajen kafa kasashe biyu masu cin gashin kan su.

Shugaba Xi Jinping ya bayyana hakan ne a Talatar nan, yayin ganawar sa da shugaban Palasdinawa Mahmoud Abbas. Ya ce samar da kasashe biyu masu cin gashin kan su, masu iyakoki da aka shata tun a shekarar 1967, da kasar Palasdinawa mai helkwata a gabashin birnin kudus ita ce hanya mafi dacewa ta cimma nasarar da ake fata. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China