in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ghana ta harba tauraron dan Adam a karon farko
2017-07-08 12:37:26 cri

Kasar Ghana ta harba tauraron dan Adam na farko wato Ghanasat 1 a jiya Jumma'a, inda ya yi nesa da doron duniya da kilomita 420.

Gidan rediyon starfm na Amurka ya ruwaito a shafinsa na yanar gizo cewa, wannan ya biyo bayan nasarar harba tauraron dan Adam da aka yi ranar 10 ga watan Yunin da ya gabata, inda a lokacin, aka harba tauraron zuwa tashar sararin samaniya ta kasa da kasa ta hanyar amfani da na'urar harba kambuna ta Spacex 11 daga tashar Kennedy dake Floridan Amurka.

An kalli yadda aka harba wannan tauraron kai tsaye a jami'ar Koforidua d132ake gabashin kasar Ghana, kuma daliban jami'ar ne suka samar da wannan shi.

Nasarar harba tauraron ya sa Ghana ta shiga tarihi a duniya, inda ta zama kasa ta farko a yankin sahara da ta harba irin wannan tauraro zuwa sararin samaniya, wanda zai ba kasar damar amfana daga fasahar tauraron dan Adam.

Tauraron na da kyamarori a tare da shi, wadanda za su iya daukar hotunan kasar tare da samar da bayanai kan abubuwan dake faruwa a yankunan ruwa na kasar. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China