Kamfaonin kasar Sin 115 sun shiga cikin jerin kamfanonin duniya mafiya girma 500 a shekarar 2017, shekaru 14 ke nan da kamfanonin kasar ke samun tagomashi na shiga cikin jerin manyan kamfanonin duniya.
Kamfanin Wal-Mart na Amurka shi ne ke kan gaba cikin jerin sunayen. Sai kamfanin samar da lantarki na kasar Sin da kamfanin mai na Sinopec suna matsayin na biyu da na uku, wadanda suke samar da kudin shiga da ya kai dala biliyan 315 da kuma dala biliyan 268 dukkaninsu a shekarar 2016.
Manyan kamfanonin na kasar Sin guda goma sun shiga sahun gaba a cikin jerin sunayen kamfanonin na duniya a karon farko, ciki har da kamfanin inshura na Anbang, da kamfanin samar da ayyukan yanar gizo na Alibaba da Tencent.
Kamfanonin na Sin sun shiga cikin hada hadar da suka hada da na internet, dillanci, harkokin kudi, makamashi, da harkar gidaje.(Ahmad Fagam)