Ali ya kara da cewa, za a gudanar da bincike tare da hukunta wadanda aka gano suna da hannu wajen kawo cikas ga yadda ake aiwatar da shari'ar da aka yanke wa Saif al-Islam Gaddafi.
Wata kungiyar 'yan tawaye ne ta ke tsare da Gaddafi, mai shekaru 45 a duniya tun shekarar 2011 a garin Zintan, da ke kudu maso yammacin birnin Tripoli. Ana zarginsa ne da tada tashin hankali da hallaka masu zanga-zanga a tarzomar da ta tashi a shekarar 2011, wadda ta yi sanadiyyar tunbuke mahaifinsa daga karagar mulki.
Wata kotu a Tripoli ta zartar da hukuncin kisa kan Saif Gaddafi, wanda a baya ake gani a matsayin wanda zai gaji mahaifinsa, an yanke masa hukuncin kisan ne tare da wasu tsoffin jami'an tsohuwar gwamnatin Libyan a shekarar 2015. Sai dai kuma, majalisar dokokin dake zamanta a gabashin kasar, ta yi wa Saif Al-Islam din afuwa jim kadan bayan yanke masa hukuncin. (Lubabatu)